17.03.2015 tarihli ihale teklif sonuçları....pdf

DOWEN COLLEGE LAGOS
DEPARTMENT OF LANGUAGES
SUBJECT: BAKAKE DA WASULAN HAUSA
CLASS: JS2
TEACHER: MRS OGUNDAMOWO
E-MAIL ADDRESS: [email protected]
SHUGABANCI
Ma’anar shugabanci
Shugabanci shine daukar nauyi jama’a da yake shugabanta kamar abubuwa rayuwa na yau da
kullum:
Lafiya,Ilimi,Hanyoyi Wuta d.s
IRE-IREN SHUGABANCI
1.
Zaman gida
2.
Zaman gandu
3.
Shugabanci a tsarin mulki
i.
Dagaci ko magaji
ii.
Hakimi
iii.
Sarki
4.
5.
Shugabanci fuskar ilimi
Shugabanci a fukar Aiki/Sanar.
ZAMAN GIDA
A wannan tsari mai gida ko Uba shine shugaban gidansa. Matansa,ya’yasa ,yaran gida masu yin
masa hidimomi suna karkashinsa a matsayin mabiya. Nauyi ciyarwa da wurin kwanciya ,tuffafi
duk ya rataya a yuwar mai gida. Shi ne zai shirya aikin da kowanne su za su yi, ya kuma tabbatar
da su yi aiki. Duk wanni abu da ake buka ta a gida shi ake tambaya, sai ya bada izini a ke yin
wannan abu a gida.
Haka kuma kare lafiyar mutane gida duk ya rataya a yuwarsa.
ZAMAN GANDU (BABBAN GIDA)
Wannan shine tsari zaman na Bahaushe na asali. A nan ana zaune ne a babban gida tare da ma
gidanta fiye da goma. Kowane da yankinsa a gida, in da yake da rukunnin iyalinsa a karkeshi
shugabancin (Uban-Gandu)
Wannan tsari gandun shugaba daya tal duk abinda ya ce ya zauna. Idan ya yanka bata
tashi. Wannan shine dattijjo mafi tsufa a gidan mafi shekaru . wannan tsohon zai kasance da nasa
rukunni tare da iyalinsa, a irin wannan gandun akan sami mutane tamanin zuwa dari. Shugaban
gandun shi ke kulla da hadin kan jama’ar gandun ,raba aikin a gidan , hakokin aure idan yara sun
kai munzulin aure ko sun so , ya kula da rigingimu da kan tashi cikin gandun ya zama alkali, ya
yi sharia. Idan ya yanka hukunci ya zaunu. Duka gandun na bin umurninsa.a irin wannan zaman,
za ka samu daga kakanni, sai ‘ya’ya da jikoki, wato duk zuriya daya ce babu bare. Wannan
zaman yan’uwantaka da kara kulla zumunci da taimakon ‘yan’uwa da hada kai. Lokacin noma
sai an yin a gandu kafin a bi gonakin sauran yan’uwa su nome.
SHUGABANCIN TSARIN MULKI
A.
UNGUWA
Gidaje suka hadu suka yi unguwa. A kan zabi shugaba guda wato “Mai-unguwa”ya dauki
shugabanci sauran’iyayen-gandu da iyalinsu. Galabi, Dagaci ko Magaji yak e zabar Maiunguwa ta hanyar ganawa da sauran jama’ar unguwar wadanda da suke da amincewa da
mutumin da za a ba wannan shugabanci. A tsarin mulki dukan ayyukan da hukuma ke so tayi sai
an bi wurin mai unguwa, shi ke yin sulhu da shirya jama’a idan rigima ta taso. . miisali na gona,
aure ko fada ko sata da dai makamantansu. Ida aka sami rasin yarjejeniya sai a gabatar da shi ga
Dagaci . Duk abinda hukuma za ta yi sai sun nemi goynbayansa.
B.
DAGACI KO MAGAJI
A kauye akan sami unguwanni dayawa da gidaje dayawa. Akan zabe shugaban wanda zai lura da
kauyen . sarki shi ke ikon nada Dagaci ko magaji. Dagaci shi zai dauki nauyin wannan kauyen.
Ta wurinsa ne talakawa zasu gabatar bukatun su zuwa hukuma. Dagaci yana dauka nauyi
taimakawa Mai’uguwaninsa. Kokarin Dagaci kullum shi ne ya kyautata rayuwar jama’arsa.
C.
HAKIMI
Hakimi shi ne shugaban gari ko kasa wanda kauyukan Dagaci suna karkashinsa. Sarki shi yake
nada Hakimi domin ya lura da mutanensa. Hakimi shi ya ke kula da kauyukan da suke cikin
yankin kasarsa. Duk abinda hukuma take bukatar jama’a su yi, shi ne zai tara Dagaci da
Maiuguwanni ya ba su umurni, hakimi a matsayin sa na shugaba shi ke kwantar da rigima ko
tarzoma da tashi a kasarsa.
D.
SARKI
Wannan shine shugaban Al’umma duka a tsarin mulki. Duk Hakimai, Dagaci, Maiunguwnni da
Talakawa suna karkashisa ne a matsayi mabiya. Sarki shi ke jagorancin jama’ar sa a kan
kowanne abu da ya shafi rayuwa. Sarki shine Baban kowa. Don haka ake ce dasu “ iyayen
jama’a
AIKIN GIDA
LITTAFI:- Fahimtar Hausa
Shafi na 43.
Tambaya: Yi bayani a kan wadannan a sarauta Hausawa
i.
Turaki
ii.
Yerime
iii.
Waziri
iv
Madaki
Send your answers to the above e-mail address.